Wata kungiyar magoya bayan APC da ke yakin neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ta yi barazanar janye goyon bayan da take ba shi bisa radin kanta, idan har tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ci gaba da kasancewa cikin tsarin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.


Kungiyar mai suna Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027, ta bayyana wannan gargadi ne cikin wata takardar korafi mai dauke da kwanan watan 25 ga Agusta, 2026, wadda ta aika wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, tare da kwafin takardar zuwa fadar shugaban kasa.


Kungiyar ta ce korafinta ya ta’allaka ne musamman kan nada Sheriff a matsayin mai kula da yakin neman zaben APC na shiyyar Arewa maso Gabas, a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar domin zaben 2027.


Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Sani Ahmad Zangina, ya ce kungiyar na nan daram kan kudirinta na ganin an sake zaben Tinubu, amma ba za ta iya ci gaba da gangamin neman masa goyon baya ga talakawa ba muddin wannan tsari bai sauya ba.