Gwamnatin Jihar Kano ta tallafa wa kusan ‘yan kasuwa 40 da gobara ta shafa a yankin Small-Scale Industrial Area da ke Dakata, da jimillar kuɗi har Naira miliyan 100.

An miƙa kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa ne a madadin Gwamnan Jihar Kano, yayin da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna matuƙar damuwa kan mummunar gobarar da ta haddasa asarar dukiya da kuma kawo cikas ga harkokin kasuwancin waɗanda abin ya shafa.

Alhaji Umar Farouk ya ce tallafin ya kasance cikar alƙawarin da Gwamnan ya ɗauka na taimaka wa ‘yan kasuwar, domin rage musu raɗaɗin asarar da suka fuskanta tare da ba su damar komawa harkokin kasuwancinsu.

Ya buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗin cikin hikima wajen farfaɗo da jarinsu, sake buɗe sana’o’insu da bunƙasa kasuwancinsu, domin su ci gaba da dogaro da kansu tare da bayar da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin jiha