Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta ce mutanen da suka bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano dukiyar Najeriya da aka wawure tare da ɓoye ta a ƙasashen waje, na iya samun lada har zuwa kashi 5 cikin 100 na ƙimar dukiyar da aka ƙwato.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yi kira ga mutanen da ke da bayanan sirri kan inda aka ɓoye kuɗaɗe da kadarorin Najeriya a ƙasashen waje da su fito su miƙa bayanan ga hukumomin da abin ya shafa.

Olukoyede ya bayyana hakan ne yayin wani taro kan laifukan tattalin arziki da aka gudanar a Cambridge, Ingila, inda ya ce a ƙarƙashin tsarin ladar, mai fallasa bayanan da suka kai ga nasarar ƙwato dukiya na iya samun tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 na ƙimar dukiyar da aka dawo da ita.

Ya kuma yi kira da a ƙarfafa matakan kare masu fallasa bayanai, yana mai cewa kariya na da matuƙar muhimmanci, musamman saboda wasu daga cikin masu bayar da bayanai na fargabar fuskantar ramuwar gayya bayan fallasa mutanen da ke da alaƙa da siyasa ko kuma masu tasiri.

Najeriya ta ƙaddamar da manufar gwamnatin tarayya ta kare masu fallasa bayanai a shekarar 2016, wadda ta tanadi lada ga mutanen da suka taimaka wajen tona asirin almundahana da kuma ɓoye ko karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kadarorinta.

Sai dai, a baya an nuna damuwa kan jinkirin biyan wasu ladan da aka yi wa masu fallasa bayanai alkawari, yayin da kuma babu wata takamaiman doka da ta tanadi cikakkiyar kariya gare su.

Sabuwar sanarwar EFCC ta sake haifar da tambayoyi kan yadda za a tabbatar da sirrin masu bayar da bayanai, tsaron lafiyarsu da kuma biyan ladan da aka yi musu alkawari.