Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin Household Prosperity and Economic Social Protection Project (HOPE-SP) da aka ƙiyasta kuɗinsa a kan dala biliyan 1, domin tallafa wa gidajen da ke cikin matsanancin buƙata da kuma taimaka wa marasa ƙarfi su samu damar dogaro da kansu.
An ƙaddamar da shirin ne a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu.
Shirin na da nufin sauya tsarin tallafin jinƙai daga bayar da tallafin gaggawa na ɗan lokaci zuwa samar da hanyoyin da za su taimaka wa jama'a su fita daga talauci tare da samun dogaro da kai.
An tsara sauye-sauyen da shirin ya ƙunsa domin inganta yadda ake gano gidajen da ke cikin buƙata da tantance waɗanda suka fi cancantar samun tallafi. Haka kuma, zai ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shirye-shiryen jinƙai da na rage talauci, tare da samar da tallafin gaggawa a lokutan matsaloli.
Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dr. Bernard Doro, ya ce ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙan shirin shi ne One Humanitarian, One Poverty Response System (OHOPRS), wanda zai haɗa shirye-shiryen agaji, tallafin zamantakewa da rage talauci cikin tsari guda na ƙasa.
Ya ce tsarin zai yi amfani da rajista guda, hanyoyin isar da tallafi na zamani, ingantaccen tsarin kuɗaɗe da bayanan zamani domin taimaka wa gwamnati yanke shawara cikin sauri da kuma tabbatar da cewa tallafi ya isa ga waɗanda suka fi buƙata.
Babban Sakatare na ma'aikatar, Olubunmi Olusanya, ya ce sauye-sauyen za su ƙara inganta haɗin gwiwa da riƙon amana, yana mai cewa babban ma'aunin nasarar shirin shi ne ganin sauyi na zahiri a rayuwar 'yan Najeriya masu buƙata.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziƙi, Abubakar Bagudu, da wakilan abokan hulɗar ƙasa da ƙasa kamar Tarayyar Turai da Bankin Duniya, sun yaba da matakin gwamnatin na ƙarfafa tsarin jinƙai da rage talauci a Najeriya.