Rundunar Sojin Nepal ta tura kusan jami’ai 2,000 domin taimaka wa aikin ceto da neman mutanen da suka ɓace sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta afku a yankunan arewacin ƙasar da ke kusa da iyakar Tibet.
Ambaliyar, wadda ta biyo bayan rugujewar wani ɓangare na kankarar tsaunin Himalaya, ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 160, yayin da daruruwan mutane suka ci gaba da kasancewa a ɓace.
Rahotanni sun ce hanyoyi da hanyoyin sadarwa da dama sun lalace ko kuma sun toshe, lamarin da ke ƙara kawo cikas ga ayyukan ceto. Akalla gadoji 19 da kusan kilomita 40 na hanyoyi ne aka lalata a wasu daga cikin yankunan da ambaliyar ta shafa.
Adadin mutanen da ba a san inda suke ba ya ci gaba da sauyawa yayin da hukumomi ke samun sabbin bayanai. A Nepal, an ruwaito ɗaruruwan mutane da suka ɓace, ciki har da 'yan yawon buɗe ido da mahajjata daga ƙasashe daban-daban. Sabbin bayanai daga Hukumar Yawon Buɗe Ido ta Nepal sun ce 570 daga cikin masu yawon buɗe ido ne aka bayyana cewa sun ɓace, ciki har da 'yan ƙasashen waje 517 daga ƙasashe 33.
A gefen iyakar Tibet da ke ƙarƙashin China, hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutane uku, yayin da ɗaruruwan wasu suka ɓace.
Hotunan bidiyo da hukumomi suka tantance sun nuna yadda gagarumin kwararar ruwa, laka da duwatsu suka ratsa yankunan da jama'a ke zaune, tare da tilasta wa mutane tserewa zuwa wuraren da suka fi tsayi domin tsira. An lalata gidaje, ƙauyuka, hanyoyi, gadoji da wasu muhimman ababen more rayuwa.
Rundunar sojin Nepal na amfani da jiragen sama masu saukar ungulu, jirage marasa matuƙa da ƙungiyoyin ceto wajen kai agaji da neman waɗanda suka ɓace, duk da cewa lalacewar hanyoyi da haɗarin ƙarin ambaliyar ruwa na ci gaba da kawo cikas ga aikin.