Wani alƙalin kotun soji ta Amurka ya sanya ranar 5 ga Yunin 2028 domin fara shari'ar Khalid Sheikh Mohammed, wanda hukumomin Amurka ke zarginsa da kasancewa babban mai tsara hare-haren 11 ga Satumba, 2001. Wannan na nufin shari'ar za ta fara kusan shekaru 27 bayan harin da ya kashe kusan mutane 3,000.

An kama Mohammed a Pakistan a watan Maris na 2003, sannan aka tsare shi a wasu wuraren sirri na CIA kafin a kai shi sansanin sojin ruwan Amurka da ke Guantanamo Bay a Cuba a shekarar 2006.

Ana zarginsa da kasancewa babban mai tsara makircin amfani da jiragen saman fasinja da aka yi garkuwa da su wajen kai hare-hare kan Cibiyar Kasuwanci ta Duniya (World Trade Center) da kuma Pentagon a ranar 11 ga Satumba, 2001.

Shari'ar za ta gudana ne tare da wasu mutane uku da ake zargi da hannu a shirin, bayan an shafe shekaru ana samun jinkiri sakamakon rikice-rikicen shari'a da batutuwan da suka shafi shaidun da za a amince da su a kotu.

Alƙalin, Lt. Col. Michael Schrama, ya ƙi amincewa da buƙatar masu gabatar da ƙara na fara shari'ar a watan Janairun 2027, yana mai cewa ana buƙatar ƙarin lokaci domin kammala muhawarar shari'a da sauran shirye-shiryen gaban kotu.

Harin 11 ga Satumba na daga cikin munanan hare-haren ta'addanci da aka taɓa kai wa Amurka, inda aka yi amfani da jirage huɗu da aka yi garkuwa da su, biyu suka buge gine-ginen World Trade Center a New York, ɗaya ya bugi Pentagon, yayin da na huɗu ya faɗi a Pennsylvania.