Gwmnatin Tarraya ta ce tufka da warwarar da jagoran ‘yan adawa kuma ɗantakaran jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ke yi kan batun mayar da tallafin mai na nuna cewa siyasa kawai ne yake son yi da batun mayar da tallafin.
A wata sanarwar da ya fitar jiya Laraba babban mai bai wa Shugaban Tinubu Shawara kan Watsa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya ce sauya maganar da Atiku ya yi sau uku cikin mako ɗaya ya nuna cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar siyasa kawai yake yi da batun dawo da tallafin mai.
Sanarwar ta ce daga farko mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya ce Atiku zai mayar da tallafi idan aka zaɓe shi kuma zai janye tallafin a hankali.
Ya ƙara da cewa daga baya wani bayani ya sake zuwa daga wani babban hadiminsa, Phrank Shaibu, wanda ya ce sanarwar Ibe wata sanarwa ce da ba a ba da izinin yinsa ba kuma wanda ke rudar da mutane game da matsayar Atiku.