Kamfanin Meta, mai mallakar Facebook da Instagram, ya amince da ɗaukar sabbin matakan da za su takaita yadda matasa a Amurka ke amfani da shafukansa.

Matakin na cikin yarjejeniyar sulhu da kamfanin ya kulla da wasu jihohin Amurka, bayan an zarge shi da haifar da illa ga yara ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.

Wani alƙali a jihar California ya amince da yarjejeniyar, yana mai cewa matakan za su taimaka wajen rage illolin da ake dangantawa da amfani da kafafen sada zumunta.

Ko da yake Meta ya musanta aikata wani laifi, kamfanin ya ce zai ƙara tsaurara hanyoyin tantance shekarun masu amfani da shafukansa, tare da sanya iyaka kan tsawon lokacin da matasa za su iya amfani da Facebook da Instagram a kowace rana.

Sai dai Meta ya ce zai biya kashi ɗaya bisa uku kacal na kuɗin sulhun idan sauran manyan kafafen sada zumunta, ciki har da YouTube da TikTok, suka amince da aiwatar da irin waɗannan takunkumai.

Wannan yarjejeniya ta zo ne yayin da ake shirin sauraron bayanin shugaban Meta, Mark Zuckerberg, kan batun.

Tun da farko, jihohin da suka shigar da ƙarar sun nemi a biya su diyya da ta kai kusan dala miliyan 200.