Shugaban Hukumar Kwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF), Ibrahim Gusau, ya yi murabus daga muƙaminsa.
Gusau ya bayyana hakan ne a yau Alhamis, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar NFF.
Murabus ɗin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da sukar yadda ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Najeriya, maza da mata, suka yi rashin kyakkyawan sakamako a 'yan shekarun nan, ciki har da rashin samun gurbin shiga gasar Kofin Duniya.
Haka kuma, rahotanni sun ce hukumomin Najeriya na gudanar da bincike kan yadda NFF ta kashe kusan Naira biliyan 17 wajen biyan albashi da sauran kuɗaɗen gudanar da harkokin 'yan wasa.
A ɓangaren gasar cikin gida kuwa, an samu korafe-korafe kan rashin biyan alƙalan wasa kuɗaɗensu daga mako na 25 zuwa mako na 38, baya ga wasu matsaloli da ake zargin sun dabaibaye harkokin hukumar.