Kusan makonni biyu ke nan ana ta ce-ce-ku-ce a Najeriya, tun bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana aniyarsa ta mayar da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Atiku na daga cikin masu ganin cewa cire tallafin man fetur na daga cikin manyan abubuwan da suka haddasa tsananin matsin tattalin arziƙin da ’yan Najeriya ke fuskanta a yanzu.

A wata tattaunawa da BBC, Atiku ya ce cire tallafin ya ƙara jefa al’umma cikin ƙunci, rashin aikin yi da matsanancin talauci.

“Ana cikin ƙunci, ana cikin rashi da rashin aikin yi. Wannan tallafin man fetur da aka janye shi ne babban abin da ya haifar da hakan. Ban taɓa ganin an sha wahala a ƙasar nan kamar wannan lokaci ba,” in ji shi.

Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani kan kalaman Atiku, inda ta ce matsayinsa na iya nuna rashin fahimtar yadda tattalin arziƙin ƙasar ke tafiya.

Sai dai Atiku ya bayyana cewa shirin da yake da shi na sake dawo da tallafin ba wai yana nufin za a ci gaba da biyan tallafin ba tare da la’akari da halin da tattalin arziƙin ƙasar yake ciki ba.

Ya ce matakin zai dogara ne da yanayin da zai tarar da ƙasar idan ya kama mulki, yana mai cewa ba zai cire ko dawo da tsarin tallafin cikin gaggawa ba.

“Ko za ka cire tallafin man fetur, ba a lokaci ɗaya za ka yi shi ba. Sai ka kyautata rayuwar talakawa kafin ka fara cirewa a hankali,” in ji Atiku.

Cire tallafin da gwamnatin Tinubu ta yi

A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da cire tallafin man fetur jim kaɗan bayan rantsar da shi.

Matakin ya haifar da tashin farashin man fetur cikin gaggawa, lamarin da ya yi tasiri kan harkokin sufuri, farashin kayan masarufi da sauran fannoni na rayuwar ’yan Najeriya.

Tun daga lokacin, Najeriya ke fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi, yayin da ake ta danganta wani ɓangare na matsin tattalin arziƙin da cire tallafin man fetur.

Da farko gwamnatin Tinubu ta yi alkawarin aiwatar da wasu shirye-shirye domin rage wa ’yan Najeriya radadin sauyin da cire tallafin ya haifar.

Sai dai sama da shekaru uku bayan matakin, wasu ’yan Najeriya na ci gaba da cewa ba su ga isasshen tasirin waɗannan matakan tallafi a rayuwarsu ba.

Naira tiriliyan 15.8 da aka samu

Ministan Kuɗin Najeriya kuma Ministan da ke Kula da Harkokin Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya ce gwamnati ta tara naira tiriliyan 15.8 daga kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur tsakanin watan Yunin 2023 da Disamban 2025.

A cewar ministan, an yi amfani da kuɗaɗen wajen raba wa jihohi ƙarin kuɗaɗe, biyan ƙarin albashi da alawus-alawus na ma’aikata, biyan basukan ƙasar da kuma gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa.

Batun cire ko dawo da tallafin man fetur na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ake tafka muhawara a kansu yayin da Najeriya ke tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.