Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Abel Enitan a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, HCSF.

Tinubu ya rantsar da Enitan ne a wani taƙaitaccen biki da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Enitan ya karɓi ragamar ofishin ne daga hannun Didi Esther Walson-Jack, wadda ta yi ritaya daga aikin gwamnati bayan ta kai shekarun ritaya na doka, wato 60.

Sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayyar ya fito ne daga jihar Osun, kuma shi ne mafi girman matsayi a cikin sakatarorin dindindin na gwamnatin tarayya.

Enitan ya shafe shekaru bakwai da watanni bakwai yana aiki a matsayin Sakataren Dindindin, inda ya yi aiki a Ma’aikatar Harkokin ’Yan Sanda, Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, da kuma Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.

An haifi Abel Enitan a ranar 12 ga Disamban 1966, kuma yanzu zai jagoranci ma’aikatan gwamnatin tarayya a matsayin shugaban ma’aikatar kula da aikin gwamnati.

Ya zama sabon HCSF ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin inganta ayyukan gwamnati da tabbatar da ingantaccen tsarin gudanar da ma’aikata.