Daraktan Hukumar Leken Asirin Amurka, CIA, John Ratcliffe, ya roƙi jami’an leƙen asirin Rasha da kada su bai wa Iran bayanan sirri da za su iya amfani da su wajen ayyukanta.
Majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun shaida wa kafafen yaɗa labaran Amurka cewa batun goyon bayan da Moscow ke bai wa Tehran na daga cikin muhimman batutuwan da Ratcliffe ya tattauna yayin wata ziyarar sirri da ya kai Moscow.
Wannan ce karon farko tun shekarar 2021 da aka bayyana a fili cewa wani daraktan CIA ya ziyarci Moscow.
Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa Ratcliffe ya gana da jami’an leƙen asirin Rasha, amma ba Shugaba Vladimir Putin ba.
Rahotanni sun ce baya ga batun Iran, Ratcliffe ya kuma tattauna da jami’an Rasha kan damuwar Amurka game da tsaron ƙasashen ƙungiyar NATO.
Sai dai hukumomin Amurka da Rasha ba su bayyana cikakkun bayanai kan abubuwan da aka tattauna ba, yayin da CIA ta ƙi yin tsokaci kan ziyarar.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana ziyarar a matsayin wani ɓangare na tattaunawar da ake yi tsakanin ƙasashen biyu, yana mai cewa irin waɗannan ganawa na iya taimakawa wajen ciyar da wasu batutuwa gaba, ciki har da ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
Sai dai Trump bai bayyana takamaiman abubuwan da aka tattauna tsakanin Ratcliffe da jami’an Rasha ba.
A cikin 'yan watannin baya-bayan nan, an samu rahotanni kan zargin cewa hukumomin leƙen asirin China da Rasha sun bai wa Iran bayanai da taimako a lokacin yaƙin da ta yi da Amurka da Isra’ila.
A nata ɓangaren kuma, Moscow ta sha zargin Washington da ƙawayenta na Turai da bai wa Ukraine taimakon leƙen asiri, tare da yin kira ga Amurka da ta dakatar da irin wannan taimako.