Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa cire tallafin man fetur ya samar da naira tiriliyan 15.8 ga ƙasar tsakanin watan Yunin 2023 da Disamban 2025.

Ministan Kuɗi kuma mai kula da harkokin tattalin arziƙi, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da rahoton ci gaban sauye-sauyen tattalin arziƙin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ya ce daga cikin naira tiriliyan 15.8 ɗin, naira tiriliyan 5.4 ne suka samu ga gwamnatin tarayya, yayin da naira tiriliyan 10.4 aka raba wa jihohi da ƙananan hukumomi ta hanyar Asusun Tarayya.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne Shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, jim kaɗan bayan rantsar da shi, yana mai cewa tsarin tallafin ya jefa kuɗaɗen gwamnati cikin matsanancin nauyi.

A lokacin, Tinubu ya ce za a karkatar da kuɗaɗen da ake kashewa wajen tallafin zuwa wasu muhimman ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen da za su amfanar da al’umma.

Sai dai tun bayan cire tallafin, ’yan Najeriya da dama sun ci gaba da neman gwamnati ta bayyana adadin kuɗaɗen da aka samu daga matakin da kuma yadda aka yi amfani da su.

A cewar Oyedele, gwamnatin tarayya ta kashe wani ɓangare na ƙarin kuɗaɗen da ta samu wajen ƙarin albashi, ƙarin mafi ƙarancin albashi da alawus-alawus ga ma’aikatan gwamnati, yayin da wani ɓangare ya tafi wajen biyan basussukan ƙasashen waje da manyan ayyukan more rayuwa.

Ministan ya ce naira tiriliyan 9.39 aka kashe wajen ƙarin albashi, mafi ƙarancin albashi da alawus-alawus, yayin da naira tiriliyan 9.37 suka tafi wajen biyan basussukan ƙasashen waje.

Haka kuma, ya ce naira tiriliyan 6.5 aka kashe wajen manyan ayyukan raya ƙasa.

Sai dai bayanin gwamnatin ya sake buɗe muhawara kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen, musamman bayan wasu masu ruwa da tsaki sun buƙaci jihohi da ƙananan hukumomi su yi cikakken bayani kan yadda suka yi amfani da naira tiriliyan 10.4 da aka raba musu.

A gefe guda, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ci gaba da sukar cire tallafin, yana mai cewa matakin ya ƙara tsananta halin rayuwa ga ’yan Najeriya.

Batun tallafin man fetur ya zama ɗaya daga cikin manyan batutuwan siyasa da tattalin arziƙi yayin da Najeriya ke tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.