Hukumar INTERPOL ta Najeriya ta ceto wasu mata biyu ‘yan ƙasar Colombia da ake zargin wata ƙungiyar masu safarar mutane ta yaudare su tare da tsare su a Najeriya.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, CSP Aniete Iniedu, ya bayyana cewa an gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan sirri daga ofishin INTERPOL da ke Bogotá a ranar 26 ga Agusta, 2026.

Matan da aka ceto su ne Maria Camila Rodas Ortiz da Yuliet Fernanda Rios Mesa.

A cewar rundunar, wasu ’yan ƙasar China da ake nema ruwa a jallo ne suka yaudari matan zuwa Najeriya, inda suka kwace musu takardun tafiya tare da tsare su ba tare da yardarsu ba.

Jami’an INTERPOL na Najeriya sun gudanar da bincike na sirri, wanda ya kai ga gano wurin da ake tsare da matan a Legas.

Daga bisani, jami’an tsaro sun kai samame tare da ceto matan lafiya. Sai dai waɗanda ake zargin sun tsere bayan sun hango jami’an tsaro suna tunkarar wurin.

Rundunar ’yan sanda ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano tare da cafke dukkan mutanen da ake zargin suna da hannu a safarar matan.

A halin yanzu, an sanya matan a wani wuri mai tsaro, yayin da ofishin jakadancin Colombia ke aiki tare da hukumomin Najeriya domin tabbatar da komawarsu ƙasarsu cikin aminci.