Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa Luanda, babban birnin Angola, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron shugabannin ƙasashen Tarayyar Afirka (AU) na musamman karo na 21.

Sanarwar da mai taimaka wa Mataimakin Shugaban Ƙasar kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar, ta ce taron zai mayar da hankali ne kan hanyoyin warware rikice-rikice da kuma samar da zaman lafiya mai ɗorewa a nahiyar Afirka.

Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasar zai gana da sauran shugabannin Afirka domin tattauna manyan ƙalubalen tsaro da nahiyar ke fuskanta, tare da duba hanyoyin da za a bi wajen dakile tashe-tashen hankula da samar da hanyoyin warware rikice-rikice cikin lumana.

Haka kuma, Shettima zai gabatar da jawabin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen taron, inda zai bayyana matsayar Najeriya kan batutuwan da za a tattauna.

A yayin taron, ana sa ran zai jaddada aniyar Najeriya ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a faɗin nahiyar Afirka.

Taron na musamman na AU na zuwa ne a daidai lokacin da nahiyar ke fuskantar ƙalubale daban-daban da suka shafi rikice-rikicen siyasa, tsaro da tashe-tashen hankula a wasu ƙasashe.