Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi wata kotun tarayya a Amurka da ta hana Ma’aikatar Shari’a ta ƙasar (DOJ), FBI da DEA fitar da wasu bayanan da suka shafi tsoffin bincike-binciken da hukumomin Amurka suka gudanar da ake dangantawa da shi.
Lamarin na da nasaba da wata ƙara ƙarƙashin dokar Freedom of Information Act (FOIA) da wani ɗan fafutukar neman gaskiya a Amurka, Aaron Greenspan, ya shigar domin samun wasu bayanan hukumomin tsaron Amurka da suka shafi Tinubu.
Greenspan na neman samun cikakken fayil ɗin FBI da wasu bayanan bincike, ciki har da bayanan da suka shafi binciken da aka gudanar a farkon shekarun 1990 da kuma wata shari’ar kwace kusan dala 460,000 a Amurka a shekarar 1993.
A cikin takardar da lauyoyin Tinubu suka gabatar wa kotu, sun yi ƙoƙarin hana ko takaita fitar da bayanan, suna masu cewa hakan na iya tauye haƙƙin sirrinsa.
Lauyoyin sun kuma yi iƙirarin cewa kasancewar wasu bayanai sun taɓa bayyana a cikin takardun jama’a ba ya nufin cewa dukkan bayanan da ke cikin fayilolin binciken ya kamata a fitar da su. Sun ce Tinubu har yanzu yana da haƙƙin kare bayanan sirri da ba a taɓa bayyana su a bainar jama’a ba.
Shari’ar ta samo asali ne daga ƙarar Greenspan da aka shigar a Kotun Gundumar Amurka ta District of Columbia a shekarar 2023, inda ya nemi bayanai daga FBI, DEA da CIA da suka shafi binciken da ake cewa ya shafi wasu mutane da kuma zargin safarar miyagun ƙwayoyi da halasta kuɗaɗen haram a farkon shekarun 1990.
A wani hukunci da kotun ta yanke a shekarar 2025, ta buƙaci FBI da DEA su sake duba wasu matakan da suka ɗauka na kin tabbatarwa ko musanta kasancewar bayanan, musamman inda bayanan binciken suka riga suka samu wani mataki na bayyana a cikin takardun gwamnati da kotu.
Sai dai sabon matakin da lauyoyin Tinubu suka ɗauka na nuni da cewa suna ƙalubalantar ƙoƙarin fitar da ƙarin bayanan da suke ganin za su iya fallasa bayanan sirri daga fayilolin binciken.
Tinubu dai ya daɗe yana musanta zargin aikata wani laifi da ya shafi safarar miyagun ƙwayoyi, kuma batun da ake gabatarwa a wannan shari’a ba ya nufin cewa kotu ta tabbatar da waɗannan zarge-zargen a kansa.
Ana ci gaba da sauraron matakan shari’ar a kotun Amurka yayin da ake takaddama kan irin bayanan da za a iya fitarwa ƙarƙashin dokar FOIA.