Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya tura Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sandan da ke kula da Shiyya ta 7, Victor Olaiya, zuwa Jihar Neja domin jagorantar aikin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a wani masallaci.

Rahotanni sun ce an sace mutanen ne a lokacin da suke gudanar da sallar Juma’a a wani masallaci da ke garin Dekara, Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja, a ranar Juma’ar da ta gabata.

Tura babban jami’in na zuwa ne yayin da hukumomi ke cewa har yanzu ba su tabbatar da ainihin adadin mutanen da aka sace ba, sannan waɗanda suka yi garkuwar ba su tuntubi gwamnati ko iyalan waɗanda abin ya shafa ba.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Neja, Obed Nuhu, ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da tattara bayanai kan lamarin.

Ya ce har yanzu babu wata tattaunawa da waɗanda ake zargin sun kai harin, yana mai cewa hukumomi na taka-tsantsan wajen guje wa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.

A cewarsa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da adadin mutanen da aka sace da kuma gano inda aka tafi da su.

An Ƙara Tura Jami’an Tsaro

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Adamu Elleman, ya ce an tura ƙarin jami’an tsaro domin tallafa wa aikin ceto.

Ya ce tawagogin yaƙi da ta’addanci, jami’an bincike na musamman, rundunar jiragen sama ta ’yan sanda da sauran jami’an tsaro na musamman na cikin waɗanda aka tura yankin.

A cewar Elleman, jami’an tsaron na aiki tare da sauran hukumomin tsaro da gwamnatin jihar domin gano inda aka tafi da mutanen tare da kuɓutar da su cikin aminci.

Elleman, wanda kakakin rundunar, Wasiu Abiodun, ya wakilta, ya kuma ce jami’an tsaro na ƙoƙarin gano waɗanda suka yi garkuwa da Sarkin Guwa, tare da ƙara tsaurara matakan tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Ana Zargin Lakurawa Da Boko Haram

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Obed Nuhu, ya ce hare-haren sun faru ne a wurare uku daban-daban a yankin.

A cewarsa, hukumomi na zargin ƙungiyoyin Lakurawa da Boko Haram da hannu a hare-haren.

Sai dai hukumomi na ci gaba da bincike domin tabbatar da waɗanda suka kai hare-haren da kuma gano ainihin adadin mutanen da aka sace.

Gwamnan Neja Ya Ba Da Umarni

Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da an ceto mutanen da aka sace cikin ƙoshin lafiya.

Gwamnan ya kuma buƙaci a ƙara ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da hare-haren suka shafa.

Gwamnatin jihar ta ce jami’an tsaro ya kamata su fara tabbatar da tsaron al’ummomin da aka kai wa hare-haren kafin a fara kai musu cikakken tallafin jinƙai.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Maurice Magaji, ya ce gwamnati za ta tantance halin da al’ummomin da abin ya shafa suke ciki tare da samar da tallafin da ya dace da zarar jami’an tsaro sun tabbatar da samun cikakken iko a yankunan.

A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyukan bincike da ceto domin gano inda aka tafi da mutanen tare da tabbatar da kubutar da su cikin aminci.