’Yan bindiga sun kashe mutane uku, sun raunata biyar tare da sace Sarkin Noman Jihar Kano, Alhaji Yusuf Nadabo Chiromawa, a wani hari da suka kai garin Chiromawa da ke Karamar Hukumar Garun Malam.


Shugaban Karamar Hukumar Garun Malam, Alhaji Aminu Salisu Kadawa, ya tabbatar da faruwar lamarin.


Kadawa ya ce, ya samu rahoton shigowar ’yan bindigar garin da misalin ƙarfe 11:00 na daren Asabar, inda suka nufi gidan Sarkin Noman tare da yin harbe-harbe kan mai uwa dawabi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane uku da raunata wasu biyar.


Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa, waɗanda suka jikkata suna asibiti domin samun kulawa, yayin da aka baza jami’an tsaro domin bin sahun ’yan bindigar da ceto Sarkin Noman.


Shugaban ƙaramar hukumar ya jagoranci zuwa asibiti inda suka shafe daren domin tabbatar da kula da lafiyar waɗanda suka jikkata.


Shugaban ya ƙara da cewa, Gwamnatin Kano za ta ƙara tsaurara matakan tsaro, tare da kira ga al’umma su dage da adduʼa tare da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai da bayanan sirri