Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC ta bayyana sunayen ’yan takarar kujerar gwamnan Jihar Kwara guda 12 da mataimakansu, domin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027.
Hakan ya ya baiwa Yan takarar damar fara shirye-shiryen yakin neman zabe gabanin babban zaɓen ƙasa.
INEC ta bayyana jerin sunayen ne a ofishin hukumar da ke Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, a ranar Asabar, inda ’yan takarar suka fito daga jam’iyyun siyasa daban-daban.
Hukumar ta bayyana Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Yakubu Danladi-Salihu, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC, yayin da Bello Mubarak Salau zai kasance mataimakinsa.
Zaɓen fidda gwani na APC, wanda tsohon Ministan Ƙasa na Harkokin Waje, Sanata Musiliu Obanikoro, ya jagoranta, ya ayyana Danladi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwamnan jam’iyyar a watan Mayu.
Jam’iyyar PDP ta tsayar da Bolakale Kawu a matsayin ɗan takararta na gwamna, yayin da Fawenu Corlenius zai kasance mataimakinsa.
Inda Jam’iyyar SDP kuma za ta fafata a zaɓen ne da Apaokagi Salahudeen a matsayin ɗan takarar gwamna, yayin da Kolawole Thawphic zai kasance mataimakinsa.
Apaokagi, wanda ya tsaya takarar kujerar Sanatan Kwara ta Tsakiya a babban zaɓen shekarar 2023, na daga cikin ’yan takarar da ke neman ƙwace mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.