Kungiyar Likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana cewa wasu daliban likitanci na fara shirin barin Najeriya zuwa kasar waje tun kafin su kammala karatunsu, sakamakon rashin kyakkyawan yanayin aiki da makoma a fannin lafiya.
Shugaban NMA, Farfesa Afekhide Omoti, ya ce wasu daliban na fara rubuta jarabawar cancantar aiki a kasashen waje tun lokacin koyon aikin likitanci, domin su samu damar yin hijira bayan sun kammala rajista.
Omoti ya ce akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta inganta albashi, tsaro, kayan aiki da jin dadin likitoci domin dakile yawan barin kasar da kwararrun ma’aikatan lafiya ke yi.
Shugaban NMA ya kuma yi gargadin cewa gwamnati na kashe makudan kudade wajen horar da likitoci, amma daga bisani su bar kasar zuwa kasashen waje, lamarin da ya ce yana jefa tsarin kiwon lafiyar Najeriya cikin hadari.