Rahoton ya ce Najeriya ce ke kan gaba a fannin zuba jarin mai da iskar gas a Afirka, wanda jimillarsa ta kai dala biliyan 221 a faɗin nahiyar.
Wannan ci gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen duniya ke faɗi-tashin neman ingantaccen makamashi, lamarin da ke sake tabbatar da matsayin Najeriya a matsayin jagorar fannin makamashi a Afirka.
Rahoton wanda kamfanin binciken makamashi na Industrial Info Resources ya fitar, ya nuna cewa a halin yanzu ana bin diddigin manyan ayyukan samar da mai da iskar gas sama da 800 a ƙasashen Afirka daban-daban.
Wannan rahoto ya nuna yadda manyan kamfanonin ƙetare ke ci gaba da amfani da albarkatun makashin da nahiyar ke da su, duk da kiraye-kirayen da ake yi na komawa ga makamashin da baya gurɓata muhalli.
Najeriya na sa ran samo sabbin hannayen jarin da ya kai tsakanin dala biliyan 30 zuwa biliyan 50 nan da shekara ta 2030, ta hanyar manyan ayyukan hakar mai da iskar gas har guda 22 a cikin teku