Jagoran Juyin Juya Hali na Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya yi gargaɗi ga ƙasashen Larabawa, inda ya bayyana cewa ƙasashen Amurka da Isra'ila na yin amfani da dabarun haifar da rarrabuwar kawuna domin raunana haɗin kan Musulmi.

A cikin wata sanarwa ta musamman da ya fitar, jagoran ya jaddada cewa maƙiya suna amfani da farfaganda da maƙarƙashiya domin ganin sun gurɓata tsarin zamantakewar al'umma, musamman bayan fuskantar ƙalubale da suka sha a fagen fama.

Tun bayan hawansa karagar mulki, sabon jagoran ya mayar da hankali wajen ƙarfafa dakarun ƙasar da kuma yin kira ga ƙasashen da ke maƙwabtaka da Iran ɗin, da su haɗa kai wajen fatattakar dakarun ƙasashen waje daga yankin Gabas Ta Tsakiya.

Duk da rahotannin da ke cewa ya sami rauni a lokacin tashe-tashen hankulan da suka gabata, gwamnatin Iran ta tabbatar wa duniya cewa yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana gudanar da ayyukansa kamar yadda ya kamata.