Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara gudanar da jarabawar da ta tsara ta kwamfuta ga mutum 2,370 da aka tantance domin ɗaukar malaman makarantun Tsangaya 500 a faɗin jihar.

Babban Sakataren Hukumar Ilimin Tsangaya ta jihar, Dokta Abubakar Maje Hamisu, ya ce mutane kusan 9,000 ne suka nemi aikin, amma aka tantance 3,500 bisa la’akari da wuraren da makarantun Tsangaya suke.

Ya bayyana hakan ne yayin da ake gudanar da jarabawar, yana mai cewa an shirya ta ne domin tabbatar da ɗaukar ƙwararrun malamai da za su taimaka wajen shirin farfaɗo da tsarin ilimin Tsangaya.

Ya ce daga cikin malaman 500 da za a ɗauka, wasu za su koyar da darussan boko kamar Turanci, Lissafi da Kimiyyar Kwamfuta, yayin da sauran malaman za su koyar da darussan addinin Musulunci.

Dokta Abubakar Maje ya ce waɗanda za su koyar da darussan addini ba za su yi jarabawar ba, sai dai za a tantance iliminsu ta wata hanya domin tabbatar da cewa sun cancanci koyar da dalibai.