Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta kama mutane 17 kan zargin aikata laifuka daban-daban, tare da ƙwato shanu, babura da wasu kayayyaki a samame da ta gudanar a sassan jihar.

Wannan na cikin sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam, ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa, an kama mutanen ne a samame daban-daban da aka gudanar a ƙananan hukumomin Malam Madori, Gwaram, Garki, Kiyawa, Taura, Birniwa, Dutse, Ringim, Miga, Kazaure da Roni, bisa zargin sata, fasa shaguna, satar shanu, lalata kadarori da fashi da makami.

Rundunar ta ce, daga cikin kayayyakin da aka ƙwato akwai shanu biyar, awaki biyu, tinkiya ɗaya, wayoyin Android tara, batiran waya 44, kwamfiyutar tafi-da-gidanka, talabijin da babura, tare da wasu kayayyaki.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu, yayin da aka miƙa batun fashi da makami ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin ci gaba da bincike tare da ƙoƙarin ƙwato wani babur da darajarsa ta kai miliyan ₦1.2.