Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a yau domin tafiya Turai, inda zai fara hutun makonni uku a matsayin wani bangare na hutunsa na shekara-shekara. 

Birnin Landan na Birtaniya ne zai kasance zangonsa na farko a wannan tafiya.

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi. 

Sanarwar ta ce ana sa ran Tinubu zai dawo Nijeriya bayan kammala hutun, domin shiga cikin harkokin yakin neman zaben 2027.