Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Yamma, karkashin Operation FANSAN YAMMA, sun yi nasarar ajalin wani babban mataimakin shugaban 'yan ta'adda tare da kwato bindigogi, alburusai da babura yayin wani samame a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina.


An gudanar da samamen ne jiya asabar yayin da dakarun Sector 2 suka kutsa cikin wasu maboyar 'yan ta'adda da aka gano a yankin.


A wata sanarwa da jami'in yada labarai na rundunar hadin gwiwar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar yau Lahadi, ya ce dakarun sun fuskanci turjiya mai tsanani daga 'yan ta'adda dauke da makamai yayin samamen. 


Sai dai Danja ya ce sun mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa 'yan ta'addar tserewa daga yankin. Ya ce bayan binciken wurin, dakarun sun tabbatar da ajalin wani dan ta'adda da ake kira Smally, wanda ke matsayin mataimaki ga fitaccen shugaban 'yan ta'adda, Kachalla Muhammadu Filani.