Karamar Hukumar Funtua ce ke kan gaba a yawan waɗanda ake zargin sun kamu da cutar mashako a Jihar Katsina, yayin da rahotannin cutar suka fito daga ƙananan hukumomi 29.

Wannan na cikin sanarwar da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Katsina ta fitar bayan taron manema labarai da aka gudanar.

Sanarwar ta bayyana cewa, bayanan da aka tattara zuwa ranar 28 ga Agustan da muke bankwana da shi sun nuna Funtua ce ke da rahotannin da suka fi yawa, sai Kankia, Bakori, Katsina, Mashi da Daura.

Mukaddashiyar Shugabar Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar, Dr. Shaima’u Kabir Abba, ta ce an fara aikin rigakafin gaggawa a mazabu 15 na Bakori, Charanchi, Funtua, Mashi da Kankia, tare da ware ƙarin cibiyoyin killace masu cutar guda uku.

Dr. Shaima’u ta ce, ƙarancin karɓar rigakafin yau da kullum da jinkirin kai masu alamomin cutar asibiti na daga cikin ƙalubalen da ake fuskanta, inda ta buƙaci jama’a su garzaya cibiyar lafiya idan suka ga alamomin cutar.