Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya reshen Jihar Ogun ta kama wata mata, Mrs. Iyabo Sowunmi, bisa zargin ƙoƙarin shigar da wasu ƙwayoyi da ake zargin haramtattu ne zuwa Cibiyar Tsare Fursunoni da ke Ibara, Abeokuta, domin ɗanta, Dare Sowunmi, wanda ake tsare bayan yanke wa hukuncin kisa.
Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya, reshen Jihar Ogun, Olayinka Odukoya, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Odukoya ya ce an kama Sowunmi da misalin ƙarfe 1:33 na rana ranar Juma'a, 28 ga Agusta, 2026, yayin da ake gudanar da binciken tsaro na yau da kullum a babbar ƙofar shiga cibiyar.
Ya ce an ɓoye abin da ake zargin “Colos” ne, wani nau’in ƙwayar roba mai tasiri ga kwakwalwa, a cikin ƙaramin leda na wani sanannen garin abin sha, kuma ana zargin an shirya kai shi ga fursunan.
Bayan gano abin, jami’an tsaro sun gaggauta tsare Mrs. Sowunmi. Bisa tsarin haɗin gwiwar hukumomin tsaro, an miƙa ta ga Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta kasa NDLEA domin gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.”
Da yake mayar da martani kan lamarin, Kwantrolan Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali na Jihar Ogun, Abioye Adesina, ya yaba wa jami’an tsaron bisa taka-tsantsan da suka nuna, da kuma bin ƙa’idojin tsaro yadda ya kamata.