Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya soki tafiyar Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zuwa Turai, yana mai cewa shugaban ƙasar ya zaɓi yin hutu ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar manyan ƙalubale.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, inda ya ce yanayin da ƙasar ke ciki na buƙatar shugaban ƙasa ya kasance tare da al’ummarsa domin fuskantar matsalolin da suke addabar su.

Ya ce duk da cewa shi ma ya taɓa yin tafiye-tafiye tare da zama a ƙasashen waje, akwai babban bambanci tsakanin tafiyar mutum mai zaman kansa da kuma ta shugaban ƙasa mai ci.

Tsadar Rayuwa Da Matsalar Tattalin Arziki

Atiku ya yi zargin cewa ’yan Najeriya na fuskantar matsanancin yanayin tsadar rayuwa, inda farashin man fetur ya ƙaru zuwa matakin da talakawa ke samun wahalar jurewa.

Ya kuma ce iyalai da dama na fuskantar matsalar ciyar da kansu, yayin da hauhawar kuɗin sufuri ke ƙara jefa jama’a cikin mawuyacin hali.

A cewarsa, tsadar sufuri ta sanya tafiya tsakanin ƙauyuka da birane ta zama babban ƙalubale ga ’yan Najeriya da dama.

Atiku Ya Yi Magana Kan Tsaro

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma yi nuni da matsalar tsaro, yana mai cewa hare-haren da ake ci gaba da fuskanta na jefa rayukan ’yan Najeriya cikin haɗari.

Ya ce a irin wannan lokaci ne shugaban ƙasa ya kamata ya kasance tare da jama’a domin nuna jagoranci da kuma tunkarar matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Atiku ya ce abin mamaki ne yadda Shugaba Tinubu ya bar ƙasar zuwa Turai a daidai lokacin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, shi ma yake wata tafiya ta aiki a ƙetare.

“Shugabanci Ya Wuce Riƙe Muƙami”

Atiku ya jaddada cewa shugabanci ba wai kawai riƙe da iko ko muƙami ba ne, illa yana buƙatar sanin lokacin da ƙasa ke buƙatar shugabanta ya kasance a gida.

Ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa wajen fahimtar irin wahalhalun da ’yan ƙasa ke ciki.

Atiku ya ce idan aka ba shi damar jagorantar Najeriya, zai yi aiki wajen samar da ƙasa mai sauƙin rayuwa ga jama’arta.

Sai dai waɗannan kalaman na Atiku na zuwa ne a matsayin suka daga babban ɗan adawar gwamnatin Tinubu, yayin da batun tafiyar shugaban ƙasar zuwa ƙetare da kuma yanayin tattalin arziki da tsaro ke ci gaba da jan hankalin jama’a.