Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ƙasashen Afirka da su ɗauki matakan ƙarfafa haɗin kai, samar da mafita daga cikin gida da kuma inganta tsaron nahiyar.
Tinubu ya bayyana waɗannan shawarwarin ne a taron musamman na Tarayyar Afirka (AU) da aka gudanar a Luanda, babban birnin Angola, inda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilce shi.
A cewar Abdulaziz Abdulaziz, ɗaya daga cikin masu magana da yawun Shugaba Tinubu, shugaban na Najeriya ya gabatar da wasu shawarwari da ya ce za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro da rikice-rikicen da ke addabar wasu ƙasashen Afirka.
1. Kawo Ƙarshen Rikice-Rikice
Tinubu ya ce ya kamata ƙasashen Afirka su ɗauki matakin ƙashin kansu wajen kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke faruwa a wasu sassan nahiyar, ciki har da Najeriya.
Ya kuma yi kira da a ƙarfafa haɗin kan ƙasashen Afirka wajen tunkarar matsalolin tsaro da ke addabar nahiyar.
Shugaban ya ce Najeriya ta goyi bayan amincewa da Shirin Aiki na Luanda, yana mai bayyana shi a matsayin wata hanya mai amfani wajen ƙarfafa matakan hana barkewar rikice-rikice.
A cewarsa, hana rikici tun kafin ya barke ya fi sauƙi kuma ya fi ɗorewa fiye da ƙoƙarin magance shi bayan ya ɓarke.
2. Rage Dogaro Da Ƙasashen Waje
Tinubu ya kuma yi kira da a rage dogaro da wasu ƙasashe wajen magance matsalolin Afirka, musamman a fannin tsaro.
A cewar Abdulaziz Abdulaziz, shugaban ya yi gargadin cewa yawan dogaro da ƙasashen waje a harkokin tsaro na iya raunana ƙoƙarin Tarayyar Afirka na hana rikice-rikice da kuma manufar cewa ’yan Afirka ne ya kamata su jagoranci warware matsalolin nahiyar.
3. Ƙarfafa Samar Da Makamai A Afirka
Shugaba Tinubu ya kuma yi kira ga ƙasashen Afirka da ke ƙera ko fitar da makamai da su ƙara haɗin gwiwa da sauran ƙasashen nahiyar wajen samar da makamai domin amfanin ƙasashen Afirka.
Ya ce irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen ƙarfafa ƙarfin nahiyar wajen tunkarar matsalolin tsaro da rage dogaro da ƙasashen waje.
Tinubu Ya Bukaci Ƙarin Haɗin Kai
A ƙarshe, Tinubu ya buƙaci shugabannin Afirka da su sake jajircewa wajen samar da mafita ta cikin gida, ƙarfafa haɗin gwiwa da kuma raba nauyin tunkarar ƙalubalen tsaro da ke addabar nahiyar.
Ya ce ƙarfafa hanyoyin magance rikice-rikice daga cikin gida da kuma haɗin kan ƙasashen Afirka na da muhimmanci wajen samar da nahiyar da za ta iya tunkarar ƙalubalen tsaro da kanta.