Fiye da mutum 2,000 ne suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP daga jam’iyyun APC, ADC da NDC a ƙaramar hukumar Nangere da ke jihar Yobe, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa an karɓi sabbin mambobin ne a wani taro da aka gudanar a Sabon Garin Nangere.
Mamban kwamitin amintattu na PDP, kuma tsohon ɗan takarar Sanatan Yobe ta Kudu, Halilu Mazagane, ya ce mutum 500 daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar sun fito ne daga APC, 1,300 daga ADC, yayin da 225 suka fito daga NDC.
Mazagane ya yi kira ga sabbin mambobin da sauran magoya bayan jam’iyyar da su kasance masu haƙuri tare da ci gaba da mara wa PDP baya a zaɓe mai zuwa.
Ya ce idan aka zaɓi PDP, jam’iyyar za ta mayar da hankali wajen samar da ayyukan yi ga matasa da kuma ƙarfafa mata.
Ya kuma buƙaci ’yan jam’iyyar da su gudanar da harkokin siyasa cikin lumana, tare da zaɓen shugabannin da suke ganin za su kawo ci gaba ga yankunansu.