Adadin mutanen da suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a Nepal ya kai 903, yayin da wasu 4,247 suka ɓace.
Hukumomin ƙasar sun tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 903, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da kuma neman dubban mutanen da har yanzu ba a san inda suke ba.
Hukumomin kula da bala’o’i na Nepal sun ce adadin waɗanda suka ɓace ya ƙaru sosai, daga mutum 2,502 da aka sanar a ranar Lahadi zuwa 4,247.
Daga cikin mutanen da ake nema akwai ’yan ƙasar Nepal 3,655 da kuma baki 592.
Ambaliyar ta yi mummunar barna a yankunan da ke kusa da iyakar Nepal da China, inda ta lalata gidaje, hanyoyi da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da ayyukan ceto da neman mutanen da suka ɓace, yayin da ake ƙoƙarin kai agaji ga waɗanda lamarin ya shafa.