Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran, IRGC, ta ce wani babban jirgin dakon mai ya kama da wuta tare da tsaya wa cak, bayan ya taka nakiyoyin ruwa guda biyu a kudancin mashigar Hormuz.
A cewar rundunar, jirgin na ƙoƙarin bin wata hanya da ta ce an haramta amfani da ita.
A wata sanarwa da kafafen yaɗa labaran Iran suka wallafa, IRGC ta ce duk wani jirgin ruwa da ya karya dokokin tsaron da ta gindaya a mashigar Hormuz na iya fuskantar irin wannan sakamako.
Har yanzu ba a bayyana sunan jirgin dakon man ba, ko kuma ƙasar da yake ɗauke da tutarta.
IRGC ta jaddada cewa dukkan jiragen ruwa da ke bi ta mashigar Hormuz dole ne su bi ƙa’idojin zirga-zirgar ruwa da rundunar sojan ruwan Iran ta gindaya.
Ta kuma gargaɗi masu jiragen ruwa da kada su bari Amurka ta rinjaye su wajen amfani da wasu hanyoyi dabam, tana mai cewa hakan na iya jefa jiragen ruwa da ma’aikatansu cikin haɗari.