Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da cewa an sayar da dukkan kujeru 3,050 da aka ware wa jihar domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2027.
Babban Daraktan Hukumar, Abubakar Ibrahim Matawalle, ya ce an samu nasarar ne bayan da hukumar ta buƙaci maniyyatan da ke buƙatar kujerun su gaggauta biyan kuɗaɗen Hajji tare da kammala dukkan takardun da ake buƙata.
Ya bayyana cewa akwai sama da mutum 200 da ke jiran samun gurbi idan wasu daga cikin waɗanda suka samu kujeru suka gaza cika sharuddan tafiya.
Matawalle ya kuma gargaɗi waɗanda suka biya kuɗin Hajji amma ba su gabatar da fasfo ɗin intanet (e-passport) ba da su gaggauta yin hakan kafin 5 ga Satumba, domin wanda ya gaza yin hakan na iya rasa kujerarsa duk da ya biya kuɗin Hajjin.
Ya ce hukumar na shirin inganta ayyukan Hajjin 2027, ciki har da rage yawan gidajen da za a saukar da alhazai a Saudiyya domin sauƙaƙa kula da su, samar da abinci, kiwon lafiya da sauran buƙatunsu.