Ministocin harkokin waje da manyan jami’an tsaro daga Turkiyya, Saudiyya da Pakistan sun gudanar da taronsu na farko a Istanbul ranar Litinin, 31 ga Agusta, kan yarjejeniyar tsaron juna da ƙasashen suka rattaba hannu a kanta a Makka.
Taron ya samu halartar manyan jami’ai da suka haɗa da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Faisal bin Farhan, da Ministan Harkokin Wajen Pakistan Muhammad Ishaq Dar, tare da manyan jami’an tsaro da hafsoshin sojojin ƙasashen uku.
Kasashen sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar Tsaron Juna ta Makka kimanin makonni uku da suka gabata a birnin Makka, a wani mataki da aka ce ya biyo bayan ƙara tabarbarewar yanayin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni sun ce yarjejeniyar na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen uku da kuma samar da matakan kariya na bai ɗaya daga duk wani hari.
A karkashin yarjejeniyar, hari kan ɗaya daga cikin ƙasashen uku za a ɗauke shi a matsayin hari kan dukkan ƙasashen, wani tanadi da ya yi kama da tsarin kariyar haɗin gwiwa da ke cikin Mataki na 5 na yarjejeniyar NATO.
Wata majiya daga Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce batutuwan da suka shafi tsaron ƙasa da ƙasa na daga cikin muhimman abubuwan da ke cikin ajandar taron.
An kuma ce damuwar da ƙasashen ke da ita kan yaƙin Iran da sauran rikice-rikicen yankin, musamman hare-haren makamai masu linzami, na daga cikin abubuwan da suka ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaron ƙasashen uku.