Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya jagoranci Sallar Gani a birnin Kano a karon farko, yayin da ɗaruruwan mahaya dawakai suka fito domin gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

Sallar Gani wata tsohuwar al’ada ce da Masarautar Kano ke gudanarwa domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W), tare da nuna al’adun gargajiya da tarihin masarautar.

A bana, an gudanar da hawan na tsawon kwanaki biyu, inda Sarkin Kano ya zagaya sassa daban-daban na birnin tare da rakiyar masu sarauta da mahaya dawakai, yayin da dubban mutane suka fito domin kallon bikin.

Hawan na bana ya samu halartar manyan baƙi da matasa da tsofaffi, lamarin da ya nuna irin muhimmancin da bikin ke da shi ga al’ummar Kano.

Rahotanni sun ce yayin gudanar da hawan, Sarkin Kano ya yi addu’o’i ga al’ummar Kano da Najeriya baki ɗaya, musamman na samun zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali.