Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya gana da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, a gefen taron Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO) da aka gudanar a ƙasar Kyrgyzstan.
Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iran, IRNA, ya ce ganawar ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi dangantakar ƙasashen biyu, sai dai ba a bayyana cikakkun bayanan tattaunawar ba.
Pakistan na taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani a tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, yayin da jami’an ƙasashen biyu ke ci gaba da ganawa akai-akai tun bayan taron da aka gudanar a Islamabad.
Shugaban China Xi Jinping, Shugaban Rasha Vladimir Putin, Pezeshkian da wasu shugabannin ƙasashe sama da goma sha biyu ne suka hallara a Kyrgyzstan domin halartar taron kwanaki biyu na SCO.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, shi ma yana cikin tawagar Pezeshkian da ta halarci taron.