Majalisar ta zartar da dokar kafa hukumar ne a zaman majalisar da aka gudanar a Ranar litinin bisa jagorancin shugaban ta Hon. Jibril Isma'il Falgore.


Hukumar da ake sa ran idan Gwamnati ta amince da ita, za ta yi aiki ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da wasu daga cikin kwamishinonin sa da shugabannin ƙananan hukumomin jihar.


Kazalika, hukumar za ta tsara yadda za a samar da cigaban tattalin arzikin jihar da inganta masana'antu tare da samar da aikin yi a tsakanin matasa