Shugaban Kasa, Bola Tinubu, ya ce ci gaban da tattalin arzikin ƙasar ke samu ya nuna cewa sauye-sauyen da gwamnatin sa ta aiwatar ya fara haifar da sakamako mai amfani.


Hakan na zuwa bayan Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya ya ƙaru da kashi 4.43 cikin ɗari a rubu’i na biyu na shekarar 2026, daga kashi 4.23 a makamancin lokacin shekarar 2025.


Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce tattalin arzikin ƙasar ya samu daidaito bayan shekaru uku na aiwatar da sauye-sauyen da ya kira masu muhimmanci.


Ya ce yanzu hankalin gwamnati zai koma wajen tabbatar da cewa ci gaban tattalin arzikin ya sauya zuwa inganta rayuwar ’yan Najeriya, musamman masu fama da ƙalubalen tsadar rayuwa.


Shugaban ya kuma bayyana cewa sauye-sauyen sun taimaka wajen inganta ajiyar kuɗaɗen Najeriya a kasashen waje.