‘Yan kasuwar man fetur da masu shigo da shi sun yi watsi da rahoton cewa matatar Dangote na shirin dakatar da sayar da fetur ga ‘yan kasuwar da ke shigo da man daga ƙasashen waje.


Sun zargi matatar da ƙoƙarin hana shigo da fetur, tare da kalubalantar ta da ta gabatar da hujjar cewa fetur ɗin da ake shigowa da shi Najeriya bai cika ƙa’idojin inganci ba.


Rahotanni sun ce matatar na nazarin takaita sayar da fetur ga manyan ‘yan kasuwa da ke ci gaba da shigo da man daga waje. 


Matatar na zargin wasu ‘yan kasuwa da haɗa fetur ɗin da suka saya daga Dangote da na waje, lamarin da take ganin zai iya haifar da ruɗani kan asalin man da aka samar a matatar.


Sai dai wasu ‘yan kasuwa sun ce Dangote na ƙoƙarin toshe hanyar shigo da fetur ne. 


A nasa bangaren, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa Masu Zaman Kansu ta Man Fetur ta Najeriya, Chinedu Ukadike, ya ce matatar Dangote tana da ‘yancin ɗaukar matakan da za su hana gurɓata ko haɗa man da ba shi da inganci.