Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa, EFCC, ta bayyana cewa ta kori sama da ma’aikatan ta 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata bisa zargin aikata rashawa da almundahanar kuɗi.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin ganawa da shugabannin kafafen yaɗa labarai da ’yan jarida.
Olukoyede ya ce, tuni aka gurfanar da biyar daga wadanda ake zargin tare da shirin gurfanar da karin wasu jami'an.
Ya ce hukumar ta kuma ƙaddamar da sabbin matakai na ƙarfafa ɗa’a da gaskiya tsakanin ma’aikatanta, ciki har da tsarin kula da kyaututtuka da kuma wajibcin bayyana kadarorin da suka wuce misali.
Shugaban EFCC ya ce ba zai yiwu ma’aikatan hukumar su yi yaƙi da cin hanci da rashawa ba, alhali su kansu suna aikata irin wannan laifi.