Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam, JNI, a Jihar Filato ta musanta rahotannin da ke cewa wata ƙungiyar Musulmi na shirin kafa hukumar Hisbah a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.
Sakataren JNI na jihar, Dr. Salim Musa Umar, ya ce babu wata ƙungiyar Musulmi da ta sanar da irin wannan shiri.
Ya bayyana cewa rahoton ya samo asali ne daga wasu hotuna da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar basirar ɗan Adam, AI, waɗanda aka yaɗa a kafafen sada zumunta.
Dr. Salim ya ce ba za a iya kafa hukumar Hisbah a hukumance a jihar ba sai da samar da doka daga Majalisar Dokokin Jihar Filato, yana mai cewa babu wata doka da gwamnatin jihar ta kafa a kan hakan.
JNI ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da masu amfani da kafafen sada zumunta da su riƙa tantance sahihancin bayanai kafin yaɗa su, domin kauce wa yada jita-jita da ka iya tayar da hankula tare da kawo barazana ga zaman lafiya a jihar.