An samu sabon ƙarin farashin man fetur a gidajen mai a sassan Najeriya tun daga farkon wannan mako, lamarin da ya ƙara wa masu motoci da sauran al’umma kuɗin da suke kashewa wajen gudanar da harkokinsu.
Rahotannin baya-bayan nan sun nuna cewa wasu gidajen mai sun ƙara farashin litar man fetur zuwa sama da ₦1,300, yayin da wasu gidajen man NNPCL a Abuja suka fara sayar da lita kan ₦1,345, daga ₦1,270 da ake sayarwa a baya.
Haka kuma, wasu gidajen mai a Legas da wasu jihohi sun yi ƙarin farashi, inda wasu ke sayar da litar man fetur kan kusan ₦1,310 zuwa ₦1,350.
Masana harkokin man fetur sun danganta ƙarin farashin da hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma ƙarin farashin da ake sayar da man fetur daga matatar Dangote ga ’yan kasuwa.
Ƙarin farashin ya sake janyo damuwa a tsakanin al’umma, musamman masu amfani da ababen hawa da ’yan kasuwa, saboda ana fargabar zai ƙara tsadar sufuri da farashin kayayyakin masarufi, tare da ƙara tsananta matsin rayuwa.