Hukumar Kula da Masu Bautar Ƙasa ta Najeriya, NYSC, ta yaba wa jami’an tsaro da sauran ƙungiyoyin da suka taka rawa wajen samun nasarar ceto ’yan bautar ƙasa 16 da aka yi garkuwa da su a jihar Kogi.

An yi garkuwa da ’yan bautar ƙasar ne a ranar 26 ga Agustan 2026, yayin da suke tafiya daga sansanin horas da masu bautar ƙasa na jihar Bayelsa zuwa Abuja, bayan kammala karatun horaswarsu.

NYSC ta musamman yaba wa Rundunar Sojin Najeriya, Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Hukumar DSS, ƙungiyoyin sa-kai na jihar Kogi da sauran waɗanda suka shiga aikin ceto, bisa ƙwarewarsu, jarumtaka, jajircewa da haɗin kai a lokacin aikin neman ’yan bautar ƙasar.

Hukumar ta kuma yaba da irin goyon bayan da Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya ke bayarwa wajen tabbatar da tsaro da walwalar masu bautar ƙasa a faɗin Najeriya.

A cikin wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta NYSC, Caroline Embu, ta fitar, hukumar ta sake jaddada ƙudurinta na kare rayuka da walwalar dukkan masu bautar ƙasa.

Ta ce NYSC za ta ci gaba da aiki tare da gwamnati da hukumomin tsaro domin ƙarfafa matakan kariya, yayin da za a sake duba wasu ƙa’idoji da hanyoyin tafiyar da ayyukan domin kauce wa sake faruwar irin wannan lamarin.