Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta rarraba jami’an ’yan sanda 250 da suka kammala horo na tsawon wata guda zuwa ƙananan hukumomin da ke kan iyaka, a mataki na ƙarfafa tsaron yankunan.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Bakori ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin bikin yaye rukuni na biyu na jami’ai 250 da suka kammala horon yaƙi da kuma sarrafa makamai.
Yan sandan da aka horar sun hadar da masu mukaman kwanstabil (Constables )da Kofur na ’Yan Sanda (Police Corporal).
Ya bayyana cewa an gudanar da horon a lokaci guda a sansanonin 9 PMF da ke Hotoro, da kuma 52 PMF da ke Challawa inda ya ce hakan na daga cikin aiwatar da unaranin Babban Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Disu, wanda a ƙarƙashin jagorancinsa ake ci gaba da inganta ƙwarewar jami’ai, ƙwarewar aiki, da kuma shirye-shiryen Rundunar ’Yan Sandan Najeriya na gudanar da ayyuka bisa kwarewa.
Bakori ya ce: “Dangane da muhimman abubuwan da muka sanya a gaba wajen gudanar da ayyukanmu, jami’ai 250 da suke kammala horonsu a yau za a tura su zuwa ƙananan hukumomin Jihar Kano da ke kan iyaka.
“Wannan tura jami’ai bisa tsari an yi ta ne domin ƙarfafa tsaron kan iyaka, ƙara yawan jami’an tsaro a al’ummomin da ke sahun gaba, da kuma inganta saurin kai ɗauki yayin samun kiran neman agaji.”
Kwamishinan ya umarci jami’an da su tabbatar sun mutunta amincewar da akayi da su. Ya kuma jaddada cewa yanayin tsaro na wannan zamani na buƙatar Rundunar ’Yan Sanda da za ta kasance mai tsauri wajen yaƙi da laifuka, amma a lokaci guda ta kasance mai tausayi da mutunta jama’a.