Wani jami’in sojin Nijar, Roger Gabriel, ya zargi wasu ƙasashen waje da hannu a bore da harbe-harben da suka faru a wani sansanin soji da ke Yamai ranar 29 ga Agusta.

Jami’in ya ce ya samu kira da saƙonni daga mutane a cikin Nijar da kuma ƙasashen waje, waɗanda suka nuna yiwuwar tsoma bakin wasu ƙasashen waje wajen tallafa wa waɗanda suka kai harin sansanin.

Roger Gabriel ya kuma yi zargin cewa wasu jami’an daga Chadi, da kuma wasu mutane masu alaƙa da tsohon shugaban Nijar, Mohamed Bazoum, sun yi magana kan yiwuwar samun taimakon ƙasashen waje da kuma amfani da dakarun musamman.

Sai dai ba a samu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da waɗannan zarge-zarge ba.

Hukumomin Nijar sun ce sun samu nasarar shawo kan lamarin, bayan da aka yi musayar wuta a sansanin.