Shugaban Amurka, Donald Trump, ya musanta wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta ABC News ta wallafa, wanda ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin tilasta Iran ta koma kan teburin tattaunawa.
Trump ya zargi ABC News da yaɗa abin da ya kira “labaran ƙarya”, yana mai cewa ba shi da sha’awar cimma wata sabuwar yarjejeniya da gwamnatin Iran.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce ya fi son yadda al’amura suke a halin yanzu, yana mai cewa Amurka na daf da samun cikakken iko kan mashigin Hormuz, yayin da tattalin arzikin Iran ke ci gaba da fuskantar matsin lamba.
Trump ya kuma yi kira ga al’ummar Iran da su tashi tsaye, inda ya tambaya: “Yaushe mutanen Iran za su tashi su yi gwagwarmaya?”
Kalaman Trump sun zo ne sa’o’i kaɗan bayan da ya bayyana hare-haren da Amurka ta kai a kusa da mashigin Hormuz a matsayin “waɗanda suka dace”, tare da gargadin cewa Washington za ta ƙara tsananta hare-haren idan Iran ta ɗauki matakin ramuwar gayya.
A nata ɓangaren, Iran ta ce hare-haren sun shafi fararen hula da ke halartar wani bikin aure a ƙauyen Kohstak Sirik, inda rahotanni suka ce aƙalla mutum biyar sun mutu, ciki har da yaro guda.
Kafofin yaɗa labaran Iran sun kuma ce sama da mutum 60 sun jikkata a harin.
Sai dai ikirarin da ɓangarorin biyu suka yi game da lamarin har yanzu ba su samu cikakken tabbaci daga majiyoyi masu zaman kansu ba.