Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi kira ga shugabannin ƙasashen Musulmi, musamman na Gabas ta Tsakiya da yankin Tekun Fasha, da su haɗa kai domin tunkarar abin da ya kira barazanar Amurka da Isra’ila.
Kamfanin Dillancin Labaran Iran, IRNA, ya ruwaito cewa Khamenei ya yi wannan kiran ne a wani saƙo da aka gabatar yayin taron Makon Haɗin Kan Musulunci.
Khamenei ya ce shugabannin ƙasashen yankin ya kamata su gano waɗanda ya kira “ainihin maƙiyansu”, su fahimci shirye-shiryensu da manufofinsu.
Ya ƙara da cewa Amurka da Isra’ila ba maƙiyan Iran da wasu ƙungiyoyin da ke adawa da su kaɗai ba ne, a cewarsa, suna kallon su a matsayin barazana ga sauran ƙasashen Musulmi na yankin Yammacin Asiya da Arewacin Afirka, har da waɗanda ke da alaƙa da su.
Saƙon ya zo ne watanni shida bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, waɗanda wasu majiyoyi na kusa da jami’an Iran suka ce sun yi sanadin mutuwar mahaifinsa, Ali Khamenei, tare da jikkata Mojtaba.
Wannan shi ne saƙo na biyu da Mojtaba Khamenei ya fitar a cikin 'yan kwanakin nan yana jaddada muhimmancin haɗin kai a cikin gida.
A wani saƙon da aka wallafa a ranar 28 ga Agusta, ya yi gargaɗi kan kalamai da ka iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Iran.