Sojojin Iran sun sanar da cewa sun kai hare-hare da jiragen sama marasa matuƙa (drones) kan wasu sansanonin sojojin Amurka da ke Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

A cewar sanarwar rundunar, an kai hare-haren kan sansanonin Dhafra da Manhad da ke UAE, yayin da aka kuma kai wasu hare-hare kan sansanin Sheikh Isa da ke Bahrain.

Iran ta ce hare-haren sun kasance ramuwar gayya ne kan hare-haren da jiragen yaƙin Amurka suka kai a baya.

Rahotanni na baya-bayan nan sun tabbatar da cewa Iran ta ƙara kai hare-hare kan wuraren da sojojin Amurka suke a wasu ƙasashen yankin, ciki har da Bahrain da Kuwait, bayan sabon zagaye na hare-haren Amurka da Iran.

Sa’o’i kaɗan kafin wannan sanarwa, Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kuma sanar da kai hare-hare kan sansanonin Amurka da ke Kuwait da Jordan.

Lamarin na zuwa ne yayin da rikicin tsakanin Iran da Amurka ke ƙara tsananta, lamarin da ya janyo fargabar faɗaɗuwar rikicin zuwa sauran ƙasashen yankin.