Cutar Mashaƙo na ci gaba da yaɗuwa a wasu sassan jihohin Filato, Katsina da Kano, inda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da janyo rashin lafiya ga wasu.
A Jihar Filato kaɗai, aƙalla mutane 23 ne suka mutu, yayin da ake zargin wasu 143 sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi daban-daban, musamman a Jos ta Arewa.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Filato, Dakta Nicholas Baamlong, ya ce mafi yawan mace-macen sun faru ne cikin makonni uku da suka gabata.
Ya ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin ɗaukar matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar, yayin da wasu marasa lafiya tara ke karɓar magani a cibiyoyin killace masu ɗauke da cutar.
Dakta Baamlong ya bayyana ƙarancin maganin antitoxin, da kuma jinkirin kai marasa lafiya asibiti, a matsayin wasu daga cikin manyan ƙalubalen da ake fuskanta wajen yaƙi da cutar.
A halin yanzu, hukumomi sun ƙaddamar da yaƙin wayar da kai ga jama'a tare da neman tallafi daga Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya, NCDC, domin samar da magunguna da kayan gwajin cutar.